Yawan korafi kullum da hangen cewa wani ya take maka hakki, bai haifar da komai sai mutuwar zuciya da musiba a cikin al’umma. A duk lokacin da mutum ya zama mai yawan korafi, to kodai rago ne, yana zaune yana jira idan biri ya tsinko dan giginya ya fadi a kasa ya dauka, ko kuwa shi ya zalunci kansa, ya ki yin abinda ya cancanta na karbo yancinsa. Ina wannan bayani ne a dangane da irin dambalwar siyasa da a ke tabkawa a jihata, jihar Taraba. Musulmai da Kiristoci, musamman matasa hankali ya gushe; a maimakon yin abinda ya kamata na ci gaban jiha, sai zage-zage da zargin juna kawai a ke yi, wanda ba zai haifar da da mai ido ba.
Da farko dai, yana da kyau mu gane cewa, rashin adalci, a tsakanin yan’uwa ne, mata da miji ne, ko a tsakanin yan kasa daya ne, baya haifar da soyayya ko zaman lafiya. Duk lokacin da mutane suka sa zalunci a tsakaninsu, to zaman lafiya da biyayya sai ya gushe; gaba da sukan juna su mamaye al’umma kamar yadda yake faruwa a kafofin social media a tsakanin mutane a yanzu. Allah ya sauwake.
A dangane da siyasar da ke gudana a yanzu kuwa, yana da wuya ka tsame na kwarai. Idan ka ji wani na kiran dan’uwansa azzalumi, Musulmi ne ko Kirista, koma mara addini, to an hana shi wata dama ne. Da zarar ya samu dama, sai ya kere kowa zalunci. Don haka, matasa su fadaka da bin maganganun mayaudaran yan siyasa, harma da miyagun malaman addini wadanda ke amfani da su don cimma wani buri nasu kawai ba don son kasa ko al’ummar ta ba.
Abu na biyu, ina so na ja hankalin mai yawan korafi, domin babbar matsala ce a cikin al’umma. Tarihi ya nuna cewa yawan korafe-korafe na nuni ne da kasalanci, rashin kwazo, da dogaro ga wani don ya ajiye ka dauka, ba wai ka tashi ka yi abu na kwarai da ya cancanta don ka samu ba. Siyasa, da ma zamantakewar dan Adam baki daya, ai tamkar wasan kwallon kafa ya ke – kowa ya shirya ya zage damtse a yi wasa babu cutarwa. Wanda ya yi nasara ya yi murna ya yi shewa, wanda kuma ya yi rashin nasara ya yi kukan zuci, wani lokaci ma ya zub da hawaye, amma kuma ya jinjina wa wanda ya yi nasara, saboda yasan a wannan karon abokin hamayyarsa ya fishi shiri da kwarewa, kuma shi Allah ya baiwa nasara, yana fatan shima gaba Allah zai bashi. Ja da baya ga rago, ba tsoro bane, shirin fada ne.
Ba sabon abu ba ne, kuma ba abun mamaki ba ne, gasa da kalubalantar juna; a na yin sa tsakanin ya’uwa, uwa daya uba daya, ko tsakanin kishiyoyi. An bayyana irin wannan zamantakewa na al’adar dan Adam a cikin karin magana da ke cewa, ‘abu a garin wani, gara a garinku, a garinku ma, gara a unguwarku, a unguwarku ma, gara a gidanku, a gidanku ma, gara a kanka. Wani mutum ne, banda Annabin Allah, ko wace al’umma ce za ta iya daukan jagoranci ta baiwa wata al’umma don tsananin ta na son waccar al’ummar?
A al’adar dan Adam, iyaye ne kawai suke iya fata har cikin ransu cewa dansu ko yarsu da suka haifa ya fisu ko ta fisu cigaba. Komabayan iyaye, duk sauran dangantaka akasin haka ne! Sai dai mutum ya baka dama ta hanyar yarjejeniyar kaima za ka bashi wata damar, ko kuwa idan ya hango dole ne ya baka wata damar don ya na tsammanin wata damar daga gare ka. Saboda haka, menene mafita ga wanda kullum ya yi zaune ya na jin cewa kullum an zalunceshi, ya fito kafafen yada labaru yana ta hauragiya da maganganu wanda zai bata dangantaka ya kuma zubar da mutunci?
Da farko dai yana da kyau mai korafi ya tsaya ya binciki kansa da kyau! Shin, shi adaline? Da ya samu dama a baya ya yi adalci? Ba ramako ne a ke yi a kansa yanzu ba? A matsayinsa na dan wasa, ya ko yi tirenin, ya bata dare, ya kware, ya goge ta yadda zai iya cin wannan gasar? Shin yana da takalmi na kwarai? Yana da juriya, da hakuri da iya wasa? Kuma yana taka wasarsa ba tare da ya cutar da wani dan wasa ba? Mai saurin fushi ne shi, alkalin wasa na iya korarsa, wanda zai iya zamowa sanadin nasara a kan tim nashi? Duk wadannan tambayoyi suna daga cikin dabaru da kwarewa ta yadda dan wasa ko kungiyar wasa za ta iya yin nasara ko akasin nasara a kan yar’uwarta.
Nasara kuma ba yana nufin zalunci ba ne, ko kuwa samun nasarar zai tabbata har abada. Idan mai korafi ya danganta wannan bayani da yadda ya ke yin siyasarsa, watakila zai iya gano ta inda ruwa ke yoyo a dakinsa. Mai korafinnan kuwa musulmi ne ko kirista, dan arewaci ne ko dan kudanci, dan kauye ne ko dan birni.
Saboda haka, idan mai korafi yana ganin an yi amfani da wani mutum mai karfi ko mai dukiya don kwace kwallo a hannunsa, to shima ya samo nashi mai karfin ko mai dukiyan ya gani shin haka abin zai cigaba da kasancewa? Ba sai na bada wannan amsa ba, mai karatu ya sani, karfi da buwaya Allah ke bada shi, kuma yana bada shi ne ga duk wanda ya so, matukar wannan mutumin ya tashi ya yi kwazo ya nema.
Ku duba dangantaka tsakanin Amurka da Rasha. Saboda kowa ya shirya, duk da kace-nace da nuna wa juna yatsa da za a yi, ba za ka ga an yi fada na zahiri ba, kuma dangantaka da hulda da juna ba a fasa ba. Saboda haka, idan kana so kaga zaman lafiya da mutunta juna tsakaninka da makobcinka, to kada ka zama malalaci, ka zama mai dogaro da kanka, kuma mai kokarin taimaka wa makwabcinka ba zaluntarsa ba.
A karshe ina kira da babban murya ga mai yawan korafi da ya tashi kuma ya farka ya yi irin abinda ya dace na zahiri bana surutan da ba gaira babu dalili ba, don ganin ya samarwa kansa gurbi a tafiyar da a ke yi, kuma ba ta hanyar gaba ko cutarwa ba. Mayaudaran yan siyasa harma da kifaffun malaman addini su guji yaudara ko maganganu da zai sa talakawa da mabiya su ji cewa kullum su a ke zalunta, suna mai kashe musu zukata. A maimakon ka cewa talaka ‘ai an zalunceka,’ kana mai tunzurashi, gara kace masa ‘ka yi sakaci ka maida kanka baya,’ ta yadda za ka zaburar dashi ya yi kwazo ya taimaki kanshi, ya taimaki iyalansa, da yan’uwansa da makwabtansa da kasarshi baki daya.
Allah ya sa mu dace duniya da lahira, amin.