Gargadi ga mai yawan korafi

Yawan korafi kullum da hangen cewa wani ya take maka hakki, bai haifar da komai sai mutuwar zuciya da musiba a cikin al’umma. A duk lokacin da mutum ya zama mai yawan korafi, to kodai rago ne, yana zaune yana jira idan biri ya tsinko dan giginya ya fadi a kasa ya dauka, ko kuwa shi ya zalunci kansa, ya ki yin abinda ya cancanta na karbo yancinsa.  Ina wannan bayani ne a dangane da irin dambalwar siyasa da a ke tabkawa a jihata, jihar Taraba. Musulmai da Kiristoci, musamman matasa hankali ya gushe; a maimakon yin abinda ya kamata na ci gaban jiha, sai zage-zage da zargin juna kawai a ke yi, wanda ba zai haifar da da mai ido ba.  Continue reading “Gargadi ga mai yawan korafi”