Shin, menene yan Najeriya ba su fahimta ba game da Muhammadu Buhari?

Irin korafe-korafen da ke faruwa a yanzu game da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, babu tantama ya yi kama da abunda ya faru a 1984, lokacin mulkinsa na farko.  Yawa-yawancin jama’a suka kosa saboda tsaurin rayuwa, daga karshe suka yi fatan Allah ya canza musu shi. Shekaru kadan bayan Allah ya kawo karshen mulkinsa, jama’a suka fahimci kuskurensu. Allah bai sake dawo da Buhari ba, sai bayan sama da shekaru talatin na gwagwarmaya, har da rasa rayuka. Sai gashi nan yau cikin kasa da shekaru biyu na mulkin Buhari, wata sabuwar kalma wai ita ‘buhariyya,’ wacce ke nufin tsaurin rayuwa, ta shigo kuddin kamusun Hausa – ma’ana, tarihi ya maimaita kansa. Wai shin a ina matsalar take ne? Kuma shin menene yan Najeriya ba su fahimta ba game da Muhammadu Buhari? 

Ko shakka babu, sanin tarihinsa da shaida na wadanda suka san shi sani na hakika, Buhari mutum ne adali mai kishin kasa da kokarin yin abunda ya kamata iya gwargwadon karfinsa. Wannan fahimtata kenan. Na yi imani Buhari na da kyakyawar nufi wa Najeriya, kuma yana iya kokarinsa wajen ceto ta. Ba laifi bane bayyana matsaloli da damuwowi da hakikanin gaskiya al’ummar Najeriya tana ciki, to amma yana da kyau mu lura cewa, ba fa gyaran kasa ba, ko gyaran gona ne, matukar ta lalace, shekaru biyu – kai ko shekaru hudu ne – sun yi kadan, iyakar yin kadan, a ce mutum ya soma dauke tsammani a kan Najeria ko shugabancin Buhari.

Babu jayayya, a matsayinsa na dan Adam, Buhari, kamar kowa, yana da nashi rauni, kuma yana da kyau masoyansa su amince da wannan. Ra’ayin shugaba Buhari irin na mazan jiya, wanda shine yasa kowa ya yi amanna dashi kuma shi ya banbanta shi da sauran batagarin yan siyasa, wani lokaci, ya kan sanya shi ya turje wa al’amura har sai ya fahimci gaskiyar lamari, kafin ya amince. Wannan ya faru a lokacin da masana suka yi ta bashi shawawar ya karya darajar Naira, wanda bai yarda ba cikin sauki har sai da kamar lokaci ya kure. Ina kyautata zaton wannan yanayi shi ya kawo jinkirin nadin jami’an gwamnatinsa har sai da ya shafe kusan rabin shekara.

A irin siyasarmu ta Afirka, a dai halin yanzu, gaskiya tsagwaro, ba koda yaushe ta ke warware bakin zaren mai jagorancin al’umma mai girma da banbance-banbance irin Najeriya. Yadda shugaba Buhari ke gudanar da siyasar fatinsa ta APC bisa dukkan alamu yana jawo tafiyar hawainiya, wanda idan bai yi hankali ba yana iya shafar gudanar da mulkinsa. Ana iya fahimtar haka, yadda al’amura ke gudana tsakaninsa da majilasar kasa da kuma yadda kyakkyawar fahimta ta kasa dorewa a fatin, har gashi yau yan Najeria sun fara tunanin wani daban ba Buhari ba. Amma fa mu gane, duk sanadin wannan shine, kokarin yin adalci  da baiwa kowa hakkinsa da barin komai ya gudana da kanshi, shi ya sanya Buhari yake yin hakan.

A ganina  a na kuskure wajen irin matakan da a ke bi don taushe zanga-zanga, misali irin wanda yan Shi’a ke yi. A na anfani da karfi fiye da kima wanda ba zai haifar da da mai ido ba. Hasali ma dai, irin wannan salo ne a ka yi anfani da shi a 1984 wajen kawar da sace-sace, barace-barace, yawon banza a kan titi, rashin da’a, rashin tsabta, da dai sauransu. Wadannan na daga cikin dalilan da yan mata ke yiwa Buhari waka, suna cewa, ‘Buhari ka cucemu, Buhari zambemu, ka hana yan mata talla – lale walale.’ Kuma shi yasa talakawa ke ganin Buhari ya cika tsanani, har suka yi Allah wadai da mulkinsa. Duk da cewa muna ganin salo ne mai tsanani, amma shin don Allah, ba wai wadannan abubuwa da makamantansu ne suka bata Najeriya ba?

Har’ila yau, bisa dukkan alamu zamananci ya soma tsere wa dattijo. Na tabbata in ba don yan Najeriya sun rasa samun kamar shi ba, da za su so a ce, Buhari na hutawa a gida, Allah ya albarkaci sauran rayuwarsa. Halin da Najeriya ta shiga kafin nasarar zaben Buhari, al’amarin ya kai gargara, ba kuma ina nufin shugaba Goodluck ne kawai sanadi ba, wanda ko shakka babu, shi ya kawo dalilan da yan Najeriya ke ganin babu mai ceto kasar sai shi. Hatta kusoshin Najeriya wadanda kowa ya sani sun tsani irin Buhari ya hau mulki, amma sun gwammace kidi da karatu, sun gwammace da yan Boko Haram su cimmusu, kamar yadda suka cimma bayin Allah a Borno da Yobe da Adamawa da Kano har da Abuja – Allah ya saka musu – sun gwammace Buhari ya cimmasu. In ba don mantuwa irin na dan Adam ba, kowa ya san irin ci gaba da a ka samu a fagen tsaro sanadiyar dawo da darajar sojojin Najeriya da Buhari ya yi. Allah ya jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya a wannan yaki da ya buwayi kowa.

Yan’uwa yan Najeriya, na yi amanna, duk da wadannan rauni da muke gani, ko in ce nake gani, bana zato har yanzu muna da kamar Buhari, kuma ba don wai ina nufin mun shiga tsaka mai wuya ba ne. Korafe-korafe ko neman canji cikin gaggawa ba shine mafita ba a yanzu. Menene mafita? Ku biyoni a makala ta gaba za ku ji dalilan da suka kai mu ga wannan hali da irin tsokaci da na yi a kansu game da yadda ya dace mu yi. Allah ya samar mana mafita da mafitarsa.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.